Barazanar yunwa a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 27.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar yunwa a Sudan ta Kudu

Yakin basasa da kuma tsananin yunwa da ake fama da shi a Sudan ta Kudu, ya janyo yawaitar al'ummar kasar da ke tsere wa zuwa gudun hijira.

Hijira sakamakon yunwa da yakin basasa a Sudan ta Kudu

Hijira sakamakon yunwa da yakin basasa a Sudan ta Kudu

Daruruwan al'ummar ta Sudan ta Kudu dai na tsere wa ne domin tsira da rayuaknsu zuwa wasu kasashe. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR ta nunar da cewa daga farkon wannan shekarar da muke ciki kawo yanzu, sama da mutane 32.000 ne daga Sudan ta Kudun suka yi kaura zuwa makwabciyar kasa Sudan, kasar da suka yi fafutukar fice wa daga cikinta a baya domin samun 'yancin cin gashin kai. Wannan adadin dai ya wuce yadda ake tsammani, abin da ya sanya hukumar ta UNHCR neman tallafin kimanin Euro miliyan 158 domin bayar da agajin gaggawa ga 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudun da suka kaurace wa matsugunansu. Rahotanni sun nunar da cewa kaso 90 cikin 100 na 'yan gudun hijirar mata ne da kanan yara da ke kwashe tsahon kwanaki biyar zuwa mako guda suna tafiya da kafafunsu kafin su kai Sudan din.