1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar shiga yajin aikin gama gari a Faransa

An shiga rana ta bakwai yau aci gaba da yajin aikin matuƙan jiragen ƙasa a Faransa.´Yan Makaranta a ƙasar na ci gaba da zanga-zangar adawa da Gwamnati, a game da wannan yajin aikin.

Ƙungiyyar ƙwadagon ta CGT na adawane da shirin Gwamnati na gudanar da garanbawul ne, a harkokin fanshone a ƙasar.

Yajin aikin a yanzu haka na ci gaba da janyowa Gwamnatin Faransa adawa daga ɓangarori daban daban. Rahotanni sun shaidar da cewa Ma´aikata da kuma Malaman Makaranta, a yanzu haka na shirye-shiryen fara wani sabon yajin aikin. Shirin hakan nada nasaba ne da adawa da shirin Gwamnati na rage yawan Ma´aikata ne. A yanzu haka dai yajin aikin matuƙan jiragen ƙasan na yiwa Faransa asarar Yuro sama da miliyan 300 akowace rana.