1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar Murar tsuntsaye

Zainab A MohammadOctober 20, 2005
https://p.dw.com/p/Bu4m
Hoto: AP

Hukumar kula da lafiya ta majalisar dunkin duniya,WHO a takaice ta bayyana damuwanta,adangane da sake bullar zazzabin muran tsuntsaya da a halin yanzu keson kasancewa ruwan dare.

Zazzabin muran na tsuntsaye wanda ya fara bayyana a nahiyar Asia a shekarata 2003,ahalin yanzu yanzu ya fara dosan wasu nahiyo da suka hadar da turai,ayayinda wasu kasashen Afrika kuwa suka fara daukan matakai na kariya.

Kakakin hukumar kula da lafiya ta mdd dake Beijing,Aphaluck Bhatiasevi,tace sake bayyana wannan mura a tsakanin alumma ,zai kasance babbar barazana ce wa rayuwar biladama.

Binciken da aka gudanar a kasar ta sin dai ya tabbatar da sake bullar murar,wanda yasa aka killace wasu tsuntsaye kimanin dubu 91,koda yake maaiklatar harkokin cikin gidan ta bada tabbacin cewa babu wanda ya kamu da wannan zazzabi,tun sake bayyanarsa.

Da bullar murar tsuntsyen a shekarata 2003 a yankin Asia dai an dauki matakan kashe dubban miliyoyin kaji da dangoginsu ,batu daya durkusar da masanaantu harkokin nama musamman a kasashen Thailand da Vietnam.Ya zuwa yanzu dai mutane 60 suka rasa rayukansu a nahiyar ta Asia daga wannan mura.

Sake bayyanan wannan annoba a kasar Sin dai,yazo ne adaidai lokacin da kasar Thailand ta sanar mutuwan wani manomi daga zazzabin murar tsuntsaye,batu kuma daya haifar da barazana a doran kasa,musamman bayan da kasashen Rasha da Romania da Turkiyya suka tabbatar da bullar kwayoyin cutar,a bincike da suka gudanar.

Abun tsoro dai inji kakakin hukumar kula da lafiya ta Mdd shine,idan kwayoyin cutan sukla yadu ajikin mutane,akwai yiwuwar yada shi daga mutum zuwa mutum,wanda kuma zai haifar da illa.

A yanzu haka dai ministocin kula da lafiya na kasashen gamayyar turai EU na gudanar da wani taron gaggawa a birnin London din kasar Britania,domin tattauna batun bullar zazzabin murar tsuntsayen,da kuma barazanar yiwuwan yaduwaerta zuwa kasashen kungiyar 25,musamman bayan tabbatar da bullarsa a Turkiyya da Romania.

Tun a jiya nedai majalisar zartarwar kungiyar EU tace tana shirin haramta shiga kasashenta 25,da kaji da dangoginsu daga kasar Rasha,sakamakon tabbatar da bullar kwaryar cutar murar tsuntsayen a kudancin birnin Moscow.

A kasar faransa dai dai harkokin cinikin kaji ya sauka da kashi 20 daga cikin 100,a kwanaki biyar da suka gabata.Ita kuwa kasar Philipines cewa tayi,zata binciki dukkan yan wasannin motsa jiki ,da zasuje gasa a kasar daga yankin kudu maso gabashin Asia.

A Amurka dai, har yanzu baa samu bullar kwayoyin cutar ba,sai dai akwai alamun daukan matakai na kariya ,saboda gudun bullarsa.

To sai dai a wannan makon cibiyar nazarin abinci da harkokin gona dake da matsuguninta a Rome,tayi gargadin cewa Afrika na cikin barazanar bullar murar tsuntsayen.

Cibiyar tace idan har an samu bullar zazzabin a gabashin Afrika,to akwai yiwuwan yaduwarsa zuwa ilahirin nahiyar,kuma musamman idan har ana iya yada ta daga mutum zuwa wani.Bugu da kari bisa ga laakari da dangantakar mutane da dabbobi a nahiyar,bazai zama abu mawuyaci cutar ta bazu ba.

A yanzu haka dai Sudan ta haramta shigowa da kaji da dangoginsu daga kasashen ketare,musamman bayan sanar da yiwuwan bullar murar tsuntsayen a gabashin Afrika.Sudan dindai na dogaro ne da sayen kaji million 15 a kowace shekara daga kasashen ketare,kasar dake kasasncewa daya daga cikin masu talauci a Afrika,sakamakon fama da yakin basasa mafi tsawon lokaci a Afrika.

Ita kuwa Afrika ta kudu dake zama kasa data fi kowace cinikin naman jimina a duniya,ta hakikance cewa babu alamun yiwuwan bullar murar tsuntsayen ,saboda cigaba da kula da bincike cikin harkokin nama.