1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar Koriya ta Arewa kan Amirka

April 14, 2017

Koriya ta Arewa ta ce za ta lalata aniyar Amirka muddin ta kai mata hari da take shirin yi. Amirka dai na hararen shirin Koriya ta arewa ne na sake kaddamar da makamin mai linzami.

https://p.dw.com/p/2bFcA
Nordkorea Machthaber Kim Jong Un
Hoto: Getty Images/AFP

Kasar Koriya ta arewa, ta yi barazanar ragargaza Amirka muddin Amirkar ta kai mata hari, da ta hasaso alamun faruwar hakan.

Rundunar sojin kasar ta yi barazanar cikin wani sakon kashedin ta a wannan Juma'ar, ta yi gargadin ne saboda bayanan da ke nunin cewa Amirka na shirin afkawa mata a fargabar ta na yiwuwar Koriyar ta aiwatar da gwajin makamin Nukiliyar ta karo na shidda.

Wani babban jami'in sojan kasar ya ce muddin Amirka ta yi abin da ya danganta shi da garaje, babu wani abin da zai hana su daukar mummunan matakin martani kan Amirkar.