Barazanar kai harin ta′addanci a Jamus | Labarai | DW | 21.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar kai harin ta'addanci a Jamus

Angela Merkel ta tabbatar da kare lafiyar al'ummar Jamus

default

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatarwa da al'ummar ƙasar cewar, gwamnati ta ƙara ƙarfafa matakanta na tsaro domin kare lafiyarsu daga barazanar ta'addanci.

"Muna fuskantar mummunan barazanar 'yan tarzoma, wanda ake gani a zahiri, kuma an jima ana magana akai. Amma ba za mu taɓa durƙusar da walwalar jama'a ba, ta irin wannan barazana. Dangane da haka ne muka ƙara matakan tsaro a dukkan sassan ƙasarmu. Jama'a na iya cigaba da gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba."

Tun daga ranar Laraba ne dai ministan harkokin cikin gida na Tarayyar Jamus ya faɗaɗa matakan tsaro, bayan ya sanar da barazanar kai hari, duk da cewar babu cikkaken bayani.

Mujallar Der Spiegel ta Jamus ɗin dai ta ruwaito cewar, akwai yiwuwar kaiwa ginin majalisar ƙasar ta Reichstag da ke birnin Berlin hari, a farkon shekara mai kamawa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Mohammad Nasir Awal