Barazanar kai hare-hare a Amurka
October 30, 2010Shugaban Amurka Barack Obama ya kudiri aniyar ragargaza ƙungiyar Al-Qaida, hakan kuwa ya biyo bayan wasu kayan kunshin da aka gano da suka taso daga Yemen a jiragen Kamafanonin UPS da Fedex,
zuwa Birnin Chicago a wasu wuraren ibada na yahudawa wanda ake kyautata zaton cewa a kwai bam a cikinsu. Ko da shike yanzu haka ƙwararu na cikin gudanar da bincikke domin tantance abinda ke cikin ƙunshin. To amma ministan cikin gida na Britaniya wanda a ƙasar ne aka gano ƙunshin da kuma Dubai ya tabbatar da cewa a kwai ababan da ka iya fashewa a cikin ƙunshin. Da ya ke magana a Washiton shugaba Barack Obama ya ce, ba zasu yi ƙasa a gwiwa ba wajan fuskantar wannan al'amari
Oton
Za mu ci gaba da ɗaukar ƙarin matakai domin kiyaye lafiyar al 'ummarmu
sanan kuma za mu cigaba da bincikken ainihin wannan ƙunshi kuma zamu dage akan ɗaukar kwakwara mataki akan ƙungiyar al-qaida
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar