1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar harin ta'addanci a Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
March 11, 2017

'Yan sanda a birnin Essen da ke yammacin Jamus sun killace wata cibiyar hada-hadar kasuwanci da ke tsakiyar garin, dangane da zargin yiwuwar kai hari na ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2Z2h1
Polizei schließt nach Terrordrohung Einkaufszentrum in Essen
Hoto: Reuters/T. Schmuelgen

Mahukuntan na Jamus sun tsaurara matakan tsaro a fadin kasar, tun bayan manyan hare-haren da suka ritsa da kasashen Faransa da Beljiyam, daura da wanda aka kai da babbar mota cikin kasuwar kirsimeti a Berlin, harin da ya kashe mutane 12 a watan Disamba.

Kakakin 'yan sanda na Essen Peter Elke ya ce, killace cibiyar rukunin shagunan na Limbecker na da nasaba da bayyanai na sirri da suka samu a jiya na yiwuwar kai hari a wurin.

"Yanzu babu bukatar gudanar da binciken mutane. Sai dai mun dauki matakin tabbatar da cewar babu kowa a cikin harabar ginin, kuma babu wanda zai shiga. Mun dauki tsauraran matakan tsaro domin muna kallon dukkan hanyoyin shige da fice na kasuwar".

Essen dai na daya daga cikin yankuna da ake da masana'antu a Jamus, mai yawan al'umma dubu 600.