Barazanar harin makaman kare dangi | Siyasa | DW | 20.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Barazanar harin makaman kare dangi

Gwamnatin Jamus ta ce ba ruwanta da barazanar harin makaman kare dangi da Chirac yayi

Jacques Chirac

Jacques Chirac

Jami’an siyasar Jamus ba su ji dadin kalaman da suka fito daga bakin shugaba Chirac na kasar Faransa ba, musamman ma a daidai wannan lokacin da ake fama da takaddama dangane da shirin makamashin nukiliya na kasar Iran. Irin wannan barazana ta amfani da makaman kare dangi daga kasashen yammaci abu ne da zai kara ba wa shuagabannin kasar Iran kwarin guiwar, ba ma kawai domin ci gaba da shirin kafa tashoshin makamashin nukiliya ba, kazalika har da kera makaman kare dangi domin tsaron kan kasarsu. Ita dai fadar mulki ta Elysee ta bayyana cewar kalaman na shugaba Chirac ba hannunka mai sanda ne ga kasar Iran ba. Amma fa shi kansa shugaban Faransar ya san tasirin da wadannan kalaman zasu yi a kasar Iran..Kuma dama masu iya magana su kan ce kowa yayi habaici a kasuwa ya san da wanda yake. Ita dai kasar Faransa tun misalin shekaru biyar da suka wuce take daukar manufofin canza dabarunta na yaki tare da sabunta fasahar jiragen ruwanta na karkashin kasa masu damarar makaman kare dangi, duk kuwa da cewar kasar bata fuskantar wata barazana tun bayan kawo karshen yakin cacar baka tsakanin kasashen gabaci da na yammacin Turai. Kasar ta kan kashe abin da ya kama kashi 10% na kasafin kudinta na tsaro akan fasahar makaman kare dangi, wadanda a halin da ake ciki yanzun ba su da wani alfanu. Sabbin makaman na kare dangi dai za a iya kai farmaki da su ne domin bannatar da wurare masu muhimmanci ga abokan adawa ba tare da an gurbata yanayin kasar yankin da lamarin ya shafa ba. Wani abin lura a nan kuwa shi ne wannan fasahar tayi daidai da wadda shugaban Amurka ke hankoronta a duk lokacin da yake batu a game da harin riga kafin domin karya alkadarin abokan adawa. Duk kuwa wanda yayi bitar shawarar shuagabannin guda biyu zai ga lamarin ya jibanci man fetur ne da iskar gas. Amma ita kanta barazanar da shugaba Chirac bata da amfani saboda ba zata yi tasiri a zukatan ‘yan ta’adda ba, wadanda hare-harensu na sare ka noke ne kuma ba su da wani sansani ko wata shelkwatar da za a iya kai wa farmaki. A saboda haka mai yiwuwa kalaman na Chirac na da nufin bayyana angizon da Faransa ke da shi ne domin a ba ta damar yin tasiri a siyasar duniya da kuma zama ja-gaba a nahiyar Turai. Wannan take-taken kuwa ya kara sanya murna ta koma ciki a game da kokarin da kasashen Turai ke yi na bin manufofin ketare da na tsaro bai daya tsakaninsu. Wajibi ne Faransar ta sake komawa taitayinta domin kuwa barazanar ta Chirac ba abin da ta haifar illa kaka-nika-yi da matsalar ‘yan ta’adda a duniya.