Barazanar barkewar cuta a sansanin 'yan Rohingya
September 22, 2017Talla
Kungiyar ta yi gargadin cewa dubban 'yan gudun hijrar na fuskantar barazana na barkewar cututtuka ganin yadda suke anfani da gurbattacen ruwa tare da zama cikin kazanta. Kungiyar ta ce baya ga ceto rayuwar wadannan mutane daga halaka akwai bukatar inganta rayuwar 'yan gudun hijra da ke tsugune a cikin tantunan don ba su taimako na kayyakin agaji da kuma tsaftace wurin zamansu.'Yan kabilar Rohingya fiye da dubu dari hudu ne suka tsallaka zuwa Bangladesh a sakamakon kisan da ake musu a kasarsu ta Myanmar sanadiyar rikicin da ya barke a watan Augusta.