Barazanar ɗumamar yanayi a Duniya | Labarai | DW | 03.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar ɗumamar yanayi a Duniya

An fara babban taron ƙasa da ƙasa kan ɗumamar yanayi a Duniya a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia. Taron dake gudana ƙarkashin laimar Majalisar Ɗinkin Duniya na samun wakilcin ƙasashe sama da 180. Taron zai samar da matsaya guda ne ga ƙasashen na Duniya dangane da yaki da matsalar ɗumamar yanayi, wacce a yanzu ke barazana ga Duniya. Ana sa ran yarjejeniyar za ta maye gurbin ta birnin Kyoto ne da wa´adinta ke ƙarewa a shekara ta 2012. Har ila taron zai kuma nemi haɗin kan ƙasashen Amirka da ƙasar Sin, wajen ganin an cimma burin da aka sa a gaba. Ƙasashen biyu dai a cewar rahotanni, sun fi kowace ƙasa a Duniya samar da gurɓatacciyar iska daga kamfanoni da Masana´antu a cikin ƙasashen na su. Kafin fara wannan taro shugaba Angela Merkel ta ce Jamus za ta gabatar da wani ƙudiri a gaban taron da zai taimaka, wajen rage gurɓatacciyar iska da Masana´antu ke fitarwa da kashi 40 cikin ɗari.