1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar ɓarkewar saban rikici a Sudan

Shugaba Omar Hasan Al -Bashir na Sudan ya bayyana barazanar ɓarkewar saban faɗa tsakanin yankunan kudu da arewancin ƙasar.

default

Omar Al-Bashir da Salva Kiir

A yayin da ya rage watani uku kacal a shirya zaɓen raba gardama na neman yancin kan yankin kudancin Sudan, alamu na ƙara nuna sake abkuwar wani saban faɗa tsakanin gwamnatin Sudan da tsafin´yan tawayen SPLM.

A wani jawabi a ya gabatar jiya birnin Syrthe na ƙasar Libiya shugaban ƙasar Sudan Omar Hasan Al Bashir ya zargi SPLM da yin fatali da wasu daga ƙa´idodin yarjejeniyar zaman lafiya da su ka rattaba wa hanu a shekara 2005.

Jawabin na shugaba Albashir ya bayyana buƙatar sake saban zama, domin tattana wannan matsaloli, matakinda yankin kudancin Sudan ya yi watsi da shi. 

A wannan mako Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tura tawaga ta mussamman a yankin Kudancin Sudan domin gani da ido inda aka kwana game da shirye-shiryen wannan zaɓe.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed Tijani Lawal