1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana ga bakar fatar Afurka a Maroko

November 7, 2006

'Yan gudun hijira bakar fatar Afurka na fama da barazana ga rayuwarsu a kasar Maroko

https://p.dw.com/p/BtxX

Wani da ake kira Patrice daga kasar Cote d’Ivoire tun misalin shekaru uku da suka wuce ya nemi mafakar siyasa a kasar Moroko, amma kuma tsdawon wadannan shekaru uku yake cikin fargaba a game da makomar rayuwarsa a wannan kasa sakamakon farautar bakar fata da matasa ‘yan kasar ta Moroko ke yi a kullu-yaumin..Patrice ya ce:

“A hakika ban san dalili ba. Da farko sun kai farmaki kan wani dan kasar Komoro. Su hudu ne kowanen su rike da wuka da adda suka far wa dan Komoron suka kwace wayarsa ta salula da katinsa na banki da kuma takardar shaidarsa ta dalibai.”

Da rana tsaka suka kai wannan harin a wata unguwa ta J4 dake birnin Rabat, wadda akasarin mazauna cikinta ‘yan rabbana ka wadata mu ne. A kuwa wannan unguwar ce kadai ‘yan gudun hijira ke da ikon samun muhalli. Aziz daga kasar Kamaru, wanda ke da shagon internet a unguwar ya gane wa idanuwansa abin da ya faru, inda ya ce:

“A wannan ranar matasan ‘yan Maroko suna cikin shirin tashin hankali. Sun kai farmaki kan wannan bakar fata suka kuma caje shi suka kwace dukkan abin dake tare da shi.”

A daidai lokacin da wannan danyyen aiki ke faruwa wasu bakar fata biyar na zaune a shagon aziz, a yayinda suka yi yunkurin kai wa dan-uwansu dauki nan take Marokawa sama da hamsin suka yi musu kawanya dukkansu rike da wukake da adduna. Patrice, wanda ya tsallake rijiya da baya, ya samu mummunan rauni a hannunsa. Ire-iren wannan hari akan bakar fata tuni ya zama ruwan dare a birnin Rabat. Aziz ya ce a halin yanzu haka bakar fata kimanin 500 ne ke fama da barazana game da makomar rayuwarsu a unguwar J4 a kowace rana ta Allah.

“Wadannan matasa da zarar sun hango bakar fata, shi ke nan likafarsu tayi gaba, saboda sun san akalla ba akasara ba zasu samu na shan taba sigari. Zasu cafke shi su caje shi su kwace salularsa da dai dukkan abin da ya sawwaka a hannunsa.”

Kyamar ‘yan gudun hijira bakar fata daga kasashen Afurka dake nkudu da hamadar Sahara tuni ya zaman ruwan dare a kasar Moroko, kuma hare-haren akansu ya fi tsananta ne a unguwannin ‘yan rabbana ka wadata mu. Masu farautar bakar fatar sun hada da matasa da kuma masu matsakaicin shekarun haifuwa, wadanda suke yawo a tituna rike da wukake, ba sa shayin kowa hatta ‘yan sanda. Su kuma bakar fatar kasancewar ba su da wata kariya sai suka rungumi kaddara, ba sa ma kai kara gun ‘yan sanda saboda ko sun yi hakan ba za a saurare su ba.