1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barayin dabbobin sun kashe mutane 37 a Zamfara

Gazali Abdou TasawaJuly 6, 2015

Harin ya wakana ne ran Asabar a garin Cigama inda maharan suka yi ta harbin kan mai uywa da wabi da ƙona gidaje da kuma kwashe dabbobi

https://p.dw.com/p/1FtgV
Nigeria Boko Harem Angriff in Damaturu
Hoto: picture-alliance/AP

A Tarayyar Najeriya wasu mutane da ake zargin ɓarayin dabbobi ne sun hallaka mutane 37 a wani kauye mai suna Cigama na cikin Jihar Zamfara a yankin arewa maso Yammacin ƙasar.Wani mutum da ya shaida lamarin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa harin ya wakana ne a ranar Asabar da ta gabata inda maharan suka dinga yin harbin kan mai uwa da wabi da cinna wa gidaje wuta dama tattare dabbobin garin.

Kana ya ce harin wanda mutane kimanin 50 ɗauke da makammai suka kawo shi na a matsayin na ramuwar gayya ga wani harin da mutanan ƙauyen na Cigama suka kai a wani ƙauye mai suna Kokeya inda suka kashe mutun biyu.Jihar Zamfara dai dama jiha ce da ta yi ƙaurin suna wajan yawan faɗace- faɗace tsakanin makiyaya da ɓarayin dabbobi.wanda hakan ne ma ya sanya al'ummar yankin kafa ƙungiyoyin sa kai na 'yan banga domin kare dukiyarsu da rayukansu.