1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baraka a kawancen jam'iyyu masu mulki a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou GAT
April 12, 2018

A Jamhuriyar Nijar ana ci gaba da mayar da martani dangane da murabus din da shugaban jam’iyyar MPN Kishin Kasa kuma ministan harkokin waje Malam Ibrahim Yacouba ya yi.

https://p.dw.com/p/2vx9f
Ibrahim Yacouba Außenminister Niger
Hoto: DW/A. M. Amadou

Makwanni da dama kenan dai da wasu rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar ta Nijar ke cewar ana zaman doya da man ja tsakanin jam’iyyar ta Ibrahim Yacouba MPN Kishin Kasa da kawancen jam’iyyun da ke mulki na MRN, biyo bayan soma nuna rashin jin dadinta game da kundin tsarin zabe da ma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato CENI inda ko a makon jiya jam’iyyar ta fitar da sanarwa tana mai caccakar kundin tsarin zaben tare da fatan ganin an sake gyaran sa muddin ana da bukatar shirya zabe na gaskiya a 2021.
 A wata fira da ya yi da wakilin DW a Yamai jim kadan bayan murabus din nasa a ranar Laraba 11 ga watan Afrilun da muke ciki, shugaban jam’iyyar ta kishin kasa ya ce Firaministan kasar  ta Nijar Briji Rafini ne ya gayyace shi ofishinsa domin ba shi wani sako daga shugaban da ke cewa ba zai iya ci gaba da aiki da shi ba a cikin gwamnatinsa. Ministan ya ce nan take ya rubuta takardar murabus din nasa dama ficewa shi da jam'iyyar tasa daga cikin kawancen jam'iyyu masu mulki na MRN. Tsohon ministan na harkokin wajen Nijar dai ya ce shi da jam’iyyarsa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kokowar ganin an shimfida tsarin zabe da ma na demokradiyya mafi inganci a kasar.

Niger Wahlen Kandidat Ibrahim Yacouba
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images