Barack Obama ya yi jawabi a kan batun tsaro | Labarai | DW | 07.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barack Obama ya yi jawabi a kan batun tsaro

Shugaban na Amirka ya yi gargadin cewar Amirka ba za ta iya kawar da ta'addanci ba kawai ta hanyar karfin soji sai da fusahohi na leken asiri:

Shugaban na Amirka ya baiyana haka ne a jawabinsa kusan na karshe da ya yi kafin ya bar mulki a kan batun tsaro sannan kuma ya kara da cewar sannan kuma ya kara da cewar:

'' Wannan shi ne ma dalilin da ya sa muka kaddamar da manya sauye-sauye ta yadda za a iya samun bayanai na siri a duniya baki daya a game da 'yan taaddar, abin da zai iya taimakawa a karya lagonsu.To sai dai shugaba Donald Trump mai shirin kama mulki a cikin watan Janairu ya yi kakkausar sukka ga shugaban da gwamnatinsa da cewar sune suka kirkiro da Kungiyar mayakan IS.