1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin duniya ya sanar da jinkirta bawa Kenya rancen dala million 260

Zainab A MohammadJanuary 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bu20
yara a ajin koyon karatu a kenya
yara a ajin koyon karatu a kenyaHoto: dpa

Bankin duniya ya jinkirta bawa kasar kenya rancen dala million 260,sakamakon damuwa da harkokin rashawa daya daibaye wannan kasa dake gabashin Afrika.

Wadannan makuddan kudade daio an amince da bawa gwamnatin kenyan ne a watan oktoban 2004 domin amfani dasu wajen inganta harkokin ilimi da gyaran bankuna da kuma tallafawa shirin yaki da cutar hiv aids.A yanzu haka dai bankin duniya ya dakatar bada wannan rancen kudi ,har sai gwamnatin Mwai Kibaki ta cikanta alkawarun data dauka na yakar Rashawa a Kenyan.

Directan Bankin duniya dake Kenya Colin Bruce ya bayyana cewa Sun dakatar da bada rancen dala millin 260 din ne sakamakon karuwan harkokin rashawa daya mamaye gwamnatin kasar.

A yanzu haka dai bankin na duniya mai matsuguni a birnin Washinton din Amurka ya tura wakilai domin gudanar bincike ,tare da gabatar da rahotan halin da Kenyan ke ciki dangane da rashawa,kafin bayar da wannan rance.

A makon daya gabata nedai idan zaa iya tunawa,Bankin duniya samu suka sakamakon amince da bawa gwamnatin Kenyan dala million 25 domin yaki da rashawa,kwanaki kalilan bayan kafofin yada labaru sun yayata yadda ministocin kasar ke fachaka da dukiyar kasa.

Akan haka hakane Mr Bruce yace bayarda da wannan rance da aka cimma yarjejeniyarsa a 2004,zai taallaka ne da sakamakon bincike kann wannan zargi da akewa gwamnatin mwai kibaki.

Akan wadannan sabbin zarge zage ne kungiyoyi kare hakkin biladama na kenya suka duka kain da nain wajen gudanar da nasu bincike kann rashawar da ake tabkawa,inda suka sanar da sakamakon bincikensu.

Maina Kiai shine shugaban hukumar kare hakkin jamaa na kasa a kenya

Oton

Mun gano cewa gwamnatin kenya ta kashe akalla million 878 wajen sayen motoci masu tsada,batu daya zame abun damuwa garemu.Saboda kashe irin waddannan makuddan kudade wajen sayen motoci kadai ,na dada tabbatar dacewa gwamnati bata da niyyan yakar rashawa ,balle rage radadin talauci da kasar ke fama dashi,kuma hakan batu ne daya shaffi hakkin jamaa.

Menene sakamakon binciken da kuka gudanar a dangane da irin motocin da aka saya.

Mun samu raho dake tabbatar daceaw a yawancin maaikatu,ministoci nada motocin aiki fiye da biyu kuma masu tsadan gaske,ayayinda sauran maaikata da dama basu da motocin da zasu tafiyar da ayyukansu dashi.

Wannan hali da Kenyan ta tsinci kanta ciki dai ya harzuka alumman wannan kasa ,musamman bayan da hukumar kare haklkin biladama ta Amnesty Inter ta sanar da rahotan dake bayyana cewa gwamnatin kasar ta kashe kimanin dala million 12.2 wajen sayan motoci masu tsa da manyan jamian gwamnatgin ke amfani dasu,ayayinda talauci ke dada durkusar da talakawa.