1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin duniya ya ce wasu kasashen Afirka na samun nasara a yaki da talauci

October 31, 2006
https://p.dw.com/p/Budx

Bankin duniya ya ce kasashen Afirka na samun ci-gaba wajen yaki da talauci to amma kokarinsu na fuskantar koma baya saboda rashin zuba isasshen jari a harkokin sadarwa da na sufuri. Bankin duniya ya ce ya kamata a ninka har sau biyu jarin da ake zubawa wajen gina hanyoyin mota, samar da wutar lantarki, inganta tashoshin ruwa. Bankin ya ce ya kamata a rubanya kudin da ake warewa wadannan bangarori da dala miliyan dubu 16 a shekara. Idan ba haka ba to Afirka ba zata cimma burin nan na raya kasa kafin shekara ta 2015 ba. Bankin na duniya ya kuma kira ga kasashe masu arziki da su cika alkawuran da suka dauka na taimakawa musammna kasashen Afirka masu arzikin man fetir don su samu kudaden shiga na euro miliyan dubu 160 tsakanin shekara ta 2000 zuwa ta 2010. A wani labarin kuma baniin duniya ya ce yawan yara da ke shiga makarantun firamare a Afirka ya karu sannan yawan yara dake mutuwa lokacin haihuwa ya fara raguwa.