1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin duniya ya bukaci kasashen G8 su cika alkawuransu ga Afrika

July 11, 2006
https://p.dw.com/p/Buqx

Shugaban bankin duniya Paul Wolfowitz yace zai tunatar da kasashen kungiyar G8 masu arzikin masanaantu game da alkawuran da sukayiwa nahiyar Afrika,game da karin agaji,ciniki da rage basusukanta.

Wolfowitz ya fadawa manema labari bayan isarsa kasar Habasha a farkon wani rangadinsa na kasashen Afrika guda 7 cewa,zai halarci taron kasahen 8,inda zai bukace su da suka alkawarin da sukayi.

Kasashen na G8 dai sunyi alkawarin ribanya taimako da suke baiwa Afrika da karin dala biliyan 50 zuwa 2010,inganta cinikaiya da kuma rage harajin kayayiyaki tare da soke basusukan da ake bin kasashe mafiya talauci a nahiyar.

Ya zuwa yanzu dai babban bankin duniya da hukumar bada lamuni ta duniya IMF sun soke basusukan da suke bin wasu kasashe 18 mafi yawansu daga Afrika.