Bangladesh ta miƙa ƙoƙon baranta ga waɗanda Sidr ta rutsa da su | Labarai | DW | 21.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bangladesh ta miƙa ƙoƙon baranta ga waɗanda Sidr ta rutsa da su

Kasar Bangaladesh ta mika ƙoƙon baranta ga ƙasashen duniya saboda neman taimakon gaggawa ga dubban yan ƙasar da suka tsira da rayukansu daga mahaukaciyar guguwan nan ta Sidr.Yanzu haka dai cututtuka sun ɓulla a yankunan da guguwar mai ɗauke da ruwan sama mai ƙarfi ta ratsa musamman a lardin Patuakhali inda guguwar ta fi ɓarna.Jami’an Majalisar Dinkin Duniya da na hukumomin agaji sun kai ziyara yankunan domin duba irin barna da guguwar ta yi tare da irin taimako da za’a iya bayarwa.Gwamnatin Bangladesh ya zuwa yanzu tace an yi mata alƙawura na kusan dala miliyan 100.