Bangladesh: Sojin Myanmar sun dasa nakiyoyi a iyakoki | Labarai | DW | 09.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bangladesh: Sojin Myanmar sun dasa nakiyoyi a iyakoki

Yayin da yan Rohingya ke cigaba da kwarara Bangladesh domin neman mafaka, hukumomin Bangladesh sun ce sojin Myanmar sun dasa nakiyoyi akan hanya.

Kasar Bangladesh ta ce sojojin Myanmar sun dasa nakiyoyi a kan iyakoki a tsakanin kasashen biyu yayin da musulmi yan kabilar Rohingya ke ci-gaba da yin kaura daga Myanmar zuwa Bangladesh. Sai dai sojojin sun musanta zargin.

A waje guda kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ta ce ta sami hujjoji kwarara da suka tabbatar da cewa sojojin Myanmar sun dasa nakiyoyi akan iyakokin.

A halin da ake ciki kuma an fara baiyana damuwa kan karancin muhimman kayayyakin bukatu da kuma barazanar barkewar cutattuka a sansanonin yan gudun hijirar na Rohingya.

Rahotanni sun ce an fara samun kokawa kan abinci da ruwan sha yayin da mata da kananan yara ke bin motoci da masu tafiya a kasa suna barar domin samun abin da za su ci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce musulmi yan Rohingya kimanin dubu 290 suka tsallaka zuwa Bangladesh a cikin makonni biyu da suka wuce.