Ban ya goyi da bayan kiran dakatar da zartas da hukuncin kisa kan Barsan da Awad | Labarai | DW | 04.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban ya goyi da bayan kiran dakatar da zartas da hukuncin kisa kan Barsan da Awad

Sabon babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya nuna goyon baya ga kiran da kwamishinar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Louise Arbour ta yiwa gwamnatin Iraqi na ka da ta zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane biyu da aka yanke musu hukuncin tare da Saddam Hussein. A cikin wani roko da ta aikewa shugaban Iraqi Jalal Talabani, misis Arbour ta sake nuna shakku game da sahihancin shari´ar da aka yiwa mutanen da suka hada da dan´ uwan Saddam wato Barsan al-Tikriti da tsohon alkali Awad al-Bandar. Daga kuma can birnin Bagadaza, gwamnati ta musanta rahotannin da aka bayar cewa a yau za´a aiwatar da hukuncin kisan akan mutanen biyu.