1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban kwana ga jagoran yaki da wariyar launin fata

December 12, 2013

Dubban dubatan mutane daga sassa daban daban, ciki har da shugabannin gwamnatocin kasashe ne, suka halarci addu'oin ban kwanan na nuna alhininsu ga marigayi Mandela.

https://p.dw.com/p/1AXsH
Nelson Mandela Abschied 12.12.2013
Hoto: Reuters

Shugabannin kasashe da na gwamnatoci daga sassa daban daban na duniya ne suka halarci addu'oin ban kwana ga jagoran fafutukar yaki da wariyar launin fata a Afirka Ta Kudu, inda daga baya kuma sauran jama'a da kuma baki daga ketare suka bi sahu wajen nuna alhininsu ga marigayi Nelson Mandela.