Ban Ki-Moon ya yi kira ga Isra′la | Labarai | DW | 17.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-Moon ya yi kira ga Isra'la

Jaddada bukatar Isra'ila ta dakatar da gine-gine a yankin Palastinawa

default

Sakataren Majalisar Ban ki-Moon shi ya bukaci kasar Isra'ila da ta dakatar da shirinta na gine ginen a wuraran share wuri zauna da ke yamma da gaɓar kogin jordan a daidai lokacin  da wa'adin da aka kayyade ke kammala a karshen wannan wata.

Mista Ban ki Monn  ya ce mun jadada kudirin Majalisar Ɗinkin Duniya na ƙasa da ƙasa akan Isara'ila wanda ya haramta ci-gaba da yin gine gine a yankunan da Palasdiniyawa suka mallaka.

Fraministan dai na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dage akan bakansane  cewa babu gudu babu ja da baya akan shirin

a ƙarshen taron da aka kamala tsakanin shugabannin yankin na gabas ta tsakiya tare da hallarta sakatariyar harkokin waje Amurka .

Mawallafi :Abdurahaman Hassane

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar