Ban Ki Moon ya shawarci aika dakarun kwantar da tarzoma a iyakokin Tchad da RCA | Labarai | DW | 21.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki Moon ya shawarci aika dakarun kwantar da tarzoma a iyakokin Tchad da RCA

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon, ya bada shawara tura dakarun shiga tsakani, a kann iyakokin Tchad da Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Ya bukaci aika tawagar sojoji dubu 11, wadda za a ɗorawa yaunin kulla da iyakokin, domin hana yaɗuwar rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Ban Ki Moon, ya bayana haɗarin da ke tattare da al´ammuran gudun hijira a kan iyakokin wannan ƙasashe.

A ɗaya wajen kuma, komitin sulhu an MDD ya amince, ƙungiyar gamayar Afrika, ta rtura dakarun kwantar da tarzoma a ƙasar Somalia.

Ƙudurin da dukkan membobin komitin sulhu su ka sa ma hannu, ya buɗawa AU ƙofar tambayar kayan aiki da kuɗaɗen da ta ke bukata, domin cimma nasara wannan aiki.

Sanarwar ta yi Allah wadai, da hare-haren da ke ci gaba da tada zaune tsaye, a ƙasar Somalia, mussamman a babban birnin Mogadiscio.