Ban Ki-Moon ya sake rokon Iraƙi da ta dakatar da hukuncin kisa | Labarai | DW | 07.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-Moon ya sake rokon Iraƙi da ta dakatar da hukuncin kisa

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya sake yin kira ga gwamnatin Iraqi da ka da ta aiwatar da hukunce hukuncen kisa bayan rataye tsohon shugaba Saddam Hussein. Kamar yadda wata sanarwar da hedkwatar MDD a birnin New York ta bayar, yanzu haka an aikewa wakilin dindindin na Iraqi a MDD da wata wasika wadda a ciki Ban Ki Moon ya nanata kiran da yayiwa gwamnatin Iraqi da ta dakatar da hukuncin kisan da kotun kolin Iraqin ta yankewa sauran jami´ai biyu na tsohuwar gwamnatin Saddam Hussein.