Ban Ki Moon ya nada Ashraf Qazi a matsayin sabon wakilin MDD a Sudan | Labarai | DW | 04.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki Moon ya nada Ashraf Qazi a matsayin sabon wakilin MDD a Sudan

A rana ta biyu ta ziyarar da yake kaiwa Sudan, babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya sake yin kira da a girmama hakin dan Adam. Ban ya kai ziyara birnin Juba, inda ya ganewa idon sa irin ci-gaban da aka samu a aikin sake gina yankin na kudancimn Sudan, bayan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da aka kulla a shekara ta 2005. A lokaci daya ya bayyana nadin sabon wakilin MDD na musamman a Sudan. Yanzu haka dai dan kasar Pakistan Ashraf Qazi zai maye gurbin dan diplomasiyar kasar NL Jan Pronk, wanda a bara gwamnatin Sudan ta kore shi bayan sukar da yayiwa rundunar sojin kasar. A dangane da rikicin lardin Darfur kuwa mista Ban ya ce yana da muhimmanci gwamnatin Sudan ta ba da cikakken hadin kai don samu nasara wanzar da zaman lafiya a yankin. Ya ce shugaba Omar al-Bashir ya nuna shirin ba da hadin kai.