1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki Moon ya gabatar da sabon shirin yiwa MDD kwaskwarima

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya himmatu wajen yiwa dokokin majalisar na yawa-yawan dogon turanci kwaskwarima cikin gaggawa musamman a bangaren da ya shafi tabbatar da zaman lafiya da kuma kayyade makamai. A hukumance Ban ya gabatarwa kasashe 192 membobin MDD shirye shiryen farko bisa wannan manufa. Yanzu haka dai zai raba aikin tabbatar da zaman lafiya zuwa sassa biyu daya game da aikin samar da zaman lafiya dayan kuma akan tsare tsare da raba kayan aiki. A halin da ake ciki MDD na da sojoji kimanin dubu 100 a yankuna dabam dabam na duniya. A lokaci daya kuma sabon sakatare janar din zai mayar da himma wajen rage yaduwa makamai a duniya.