1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya tashi da 'yan kasuwa a Mali

Abdul-raheem Hassan
November 6, 2017

Wata motar safa makare da 'yan kasuwa da ke hanyarsu ta cin kasuwar mako ta tarwatse a arewacin kasar, inda akalla mutane hudu suka mutu nan take yayin da wasu da dama a cikin motar suka jikata.

https://p.dw.com/p/2n778
Somalia Mehrere Tote bei Anschlag mit zwei Fahrzeugbomben in Mogadischu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Jami'an 'yan sanda da wasu hukumomin da ke yankin da bam din ya tashi sun tabbatar wa kamfanin dillacin labarun AFP faruwar al'amarin a ranar Litinin. Sojoji da ke ayyukan sintiri sun ce motar safa din ta tunkudi nakiyar da aka dasa kusa da garin Ansogo da ke da tazarar kilomita 100 daga Gao.

Wasu mazauna yankin na zargin 'yan ta'adda da dasa bam din da nufin daukar fansa kan mutanen yankin da ke bankada sirrinsu ga jami'an tsaro. A tun shekara ta 2012 ne dai 'yan tawayen da ake alakanta su da kungiyar Al-Qaeeda suka mamaye gandun dajin da ke arewacin Mali.

To sai dai a shekarar 2015 gwamnatin Mali da Majalisar Dinkin Duniya sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da shugabannin 'yan tawayen Tuareg da zummar raba gari da 'yan ta'adda.