Bam ya fashe a Jakarta | Siyasa | DW | 09.09.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bam ya fashe a Jakarta

A bisa ayyukan yan taadda a yau wani Bam ya fashe a jakarta tare da hallaka mutane 8 baya ga raunata sama da dari da sittin

default

Kamar dai yarda jamian yan sandan kasar suka ce babu ko shakka kungiyar Jammaa Islami wacce keda alaka da kungiyar Alqaida ce keda hannu cikin wannan danyen aikin na yau .Sun dai tabbatar da cewa an lalata wannan ofishin dake cikin kasar ta Indonesiya a sanadiyar wannan bam din daya tashi a yau Jim kadan bayan tashin wannan bam din sai hayaki ya murtuke sararin samaniya tare da haifar da dimuwa ga jammaaar dake kusa da ofishin na jakadancin kasar ta australiya a Jakarta .Kamar dai yarda babban jamiin yan sandan kasar yace baya shakkun cewa wani dan kasar Malysia kuma da kungiyar JI ne mai suna Azahiri Hussain wanda rahotanni ke cewa yana iya kera bama bamai ya haifar da wannan yamutsi na yau .Tun ba yau ba dai ake farautar wannan mutumin bayan da aka sami hatsarin Bali a shekara ta 2002 .Yace a bisa binciken dai ya tabbatar da cewa shine keda hannu a cikin wannan batu kuma a yanzu haka jamian yan sanda na cigaba da bincike kann wadannan yayan kungiyar ta JI a fadin kasar baki daya ..Idan dai baa mantaba a kalla sama da mutane 202 ne suka mutu a cikin hatsarin na tsibirin Bali a ayayin da mutane da dama suka sami munannan raunika .A cikin hatsarin dai har da yan kasar Austariliya 88 ..Wannan hatsarin na yau dai yazo kusaci da lokacin da kasar ta Indonesiya zata gudanar da zabe a zagaye na biyu a wannan watan a yayin da kasar ta Australia zata gudanar da nata zaben a watan gobe idan Allah ya kaimu ..Tun ba yanzu ba dai Amurka da kasar ta australiya sukace yan tawayen ka iya kai farmaki ga kasar ta indonesiya a yan kwanakin nan ..Wadanda suka ganewa idansu yarda lamaRIN YA FARU SUN RUWAITO CEWA BAYAN FASHEWAR WANNAN Bam DIN DAI YA KASANCE TAMKAR WATA GIRGIZAR KASA CE TA FARU A SANSANIN DA ABUN YA FARU :.Wata majiya daga maaikatar kiwon lafiya ta kasar tace mutane 8 sun mutu a yayin da 168 suka sami mumunan raunia a cikin wannan hatsarin na yau alhamis ..Wannan rikicin dai ya faru ne da safiyar nan ta yau inda a yanzu komai ya tsaya cik a dangane da wannan yamutsin ..A bisa wannan halin da kasar ta fada a ciki kuwa shugaban Kasar Megawati Sukarniputri ta katsa wata ziyara data kai can Kasar Brunei domin halartar bikin babban Da ga Sarkin kasar inda ake cigaba da baje kolin Dukiya .Ta dai tabbatar da aniyar gwamnatin ta na cigaba da yaki da yan taadda a cikin kasar baki daya ..A mayar da martani kuwa kasar ta Australiya tace wannan farmakin nada nufin dakusar da yan kasar ne dake cikin kasar ta indonesiya a halin yanzu ..tUni dai PM John Howard yace ko kadan Gwamnatinsa ba zata mika wuya ba ga yan taadda a duk inda suke a doron kasa ba ..A hannu guda dai kungiyar gamaiyar Turai alla wadai da wannan farmaki da cewa yan tawaye na neman daukar matakin mayar da hannun agogo baya

 • Kwanan wata 09.09.2004
 • Mawallafi Mansour bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvgb
 • Kwanan wata 09.09.2004
 • Mawallafi Mansour bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvgb