1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ta fashe Port Harcourt na yankin Niger Delta

Rahotani daga yankin Niger Delta,a Tarayya Nigeria, sunce a ƙalla mutane 3 sun rasa rayuka, a sakamakon tarwastewar wata Bom, a cikin barikin soja, ta Patakot.

Ƙungiyar neman yancin Niger Delta Mend,ta bayyana ɗaukar alhakin dassa wannan bam, da nufin firgitar da kampanonin haƙar man Petur nan yankin.

Sannan Mend ta ce wannan somin tabi ne domin a yanzu hak ata na shirye shiyren kai karin wassu haren, tare da yin garkuwa da jami´ai kamapanonin man petur.

Wani soja da ya ganewa idonsa, assara da Bom din ta jawo ya ce motoci da dama sun salwanta,sannan an bayan mutane 3, da su ka rasa rayuka, da dama, sun ji mumunan raunuka kuma a halin da ake ciki, su na kwace a assibitocin soja, rai kwakai mutu kwakwai.