Bala´in Guguwar Sidr a Bangladesh | Labarai | DW | 19.11.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bala´in Guguwar Sidr a Bangladesh

Ƙananan jiragen soji a ƙasar Bangladesh na ci gaba da aikin jigilar kayan masarufi ga waɗanda bala´in guguwar Sidr ta afkawa.Hakan dai ya biyo bayan yadda ambaliyar ruwa ke ci gaba da mamaye yankin da wannan annobar ta faɗawane.Guguwar dake tafiya nisan kilomita 250 cikin sa a guda, a yanzu haka tayi asarar rayuka sama da dubu biyu. Haka kuma Guguwar tayi sanadiyyar gidajen kwana masu yawan gaske.Tuni ƙungiyyar Tarayyar Turai ta bawa Bangladesh taimakon Yuro miliyan 1.500 ta fuskar agajin gaggawa, inda Jamus tayi alƙawarin ƙarin Yuro dubu ɗari biyar.

 • Kwanan wata 19.11.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CIlV
 • Kwanan wata 19.11.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CIlV