Bala′in gobarar daji a Rasha | Labarai | DW | 07.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bala'in gobarar daji a Rasha

Ƙasar Rasha na fuskantar bala'in gobarar daji

default

Birnin Moscow tirniƙe da hayaƙi.

Ƙasar Rasha na fiskantar masifar wutar daji mafi girma a tarihinta, inda hakan ya tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu a Moscow, babban birnin ƙasar , inda mutane ke sa ƙyalle don rufe hancinsu, yayin da hayaƙin da ke tirniƙe birnin ya ruɓanya har sau biyar. Yanzu haka dai wutar ta yaɗu zuwa tsakiyar ƙasar, yayin da iska mai ƙarfi ke ƙara rura ta, inda yanzu haka aƙalla mutane 52 suka mutu. An sauya wa jiragen sama dake sauka a birnin Moskow hanya don rashin kyaun yanayi. Yanzu haka ana nuna damuwa a ƙasar saboda cewa wutar ta doshi rumbun makaman nukiliyar ƙasar. Mahukuntan ƙasar suna ƙara damuwa bisa yadda wutar ta nufaci yankin yammacin ƙasar ida aka taɓa fiskatar matsalar tashin sindarin haɗa nukilya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita Halima Balaraba Abbas