1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bala'in Girgizar Kasa Da Ambaliyar Ruwa A Asiya

Jamus ta ware tsabar kudi Euro miliyan daya domin tallafa wa mutanen da bala'in girgizar kasa da almbaliyar ruwa ya rutsa da su a Asiya

Girgizar kasa da ambaliyar ruwa a Asiya

Girgizar kasa da ambaliyar ruwa a Asiya

Tun a jiya lahadi ne gwamnatin Jamus ta ware tsabar kudi Euro miliyan daya domin taimaka wa yankunan da bala’in na girgizar kasa da ambaliyar ruwa ya shafa. Kungiyoyin taimako guda goma da suka yi hadin guiwa a karkashin matakin da suka kira "Taimako Daga Jamus" sun ce tuni suka gabatar da wannan mataki bisa manufa, inda jirgin farko ya tashi daga filin jiragen saman Düsseldorf a jiya da dare dauke da kayan taimako zuwa yankin. A lokacin da yake bayani game da haka, wani jami’in kungiyar taimako ta Humedica da ake kira Wolfgang Groß nuni yayi da cewar:

Matsalar dake akwai a game da irin wannan bala’in daga Indallahi shi ne tabarbarewar dukkan hanyoyi na kiwon lafiya. A saboda haka muka hada dukkan magungunan da ake bukata Ya-Allah na tari ne ko mura ko jiri ko zazzabin cizon sauro da dai shauransu. Kazalika muna dauke da na’urar daukar hotunan X-Ray domin tantance cututtukan da mutane ke dauke dasu da sauran magungunan da suka shafi cututtuka masu saurin yaduwa tsakanin jama’a.

Kawo yanzun dai ma’aikatar harkokin wajen Jamus a birnin Berlin ba ta da wani cikakken bayani a game da ko shin akwai Jamusawa a tsakanin wadanda bala’in ya rutsa dasu. Amma rahotanni masu nasaba da kamfanonin sufuri da yawon bude ido sun ce akwai dubban Jamusawa dake yawon shakatawa a wadannan yankuna a daidai lokacin da bala’in ya afku. Rahotannin da aka bayar a hukumance sun ce baki masu yawon shakatawa kimanin 70 ne aka tsinci gawawwakinsu a kasar Sri Lanka, kuma akwai wasu Jamusawan su hudu da ba a san makomarsu ba a yankin kudancin tsuburin na Sri Lanka. A can kasar Thailand kuwa an kiyasce cewar akalla kashi daya bisa hudu daga cikin gawawwaki 460 da aka tsinta, baki ne dake yawon bude ido. Ba kuwa wani takamaiman bayani game da kon shin har da Jamusawa a tsakaninsu, saboda akwai dubban mutanen da ba a san makomarsu ba. Bugu da kari kuma hanyoyin sadarwa duk sun tabarbare a yankunan da bala’in ya rutsa dasu. Tuni dai ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta bude sabbin layukan tarfo na gaggawa, a nan cikin gida da kuma kasashen da lamarin ya shafa, domin samun saukin taimaka wa Jamusawa masu yawon shakatawa da kuma danginsu. Kamfanonin sufuri da yawon shakatawa na Jamus sun tura jiragen sama zuwa Thailand da Sri Lanka da sauran tsuburan da bala’in ya rutsa dasu domin kwaso Jamusawan zuwa gida.