Bala′in garin Duisburg | Labarai | DW | 26.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bala'in garin Duisburg

An fara bincike kan turereniyar da ta auku a Duisburg ta Jamus

default

Ma'aikatan ceto sun yi bakin ƙoƙarin kai ɗauki

Wasu alƙalan ƙasar Jamus sun fara gudanar da bincike domin gano musababbin turereniyar da ta hallaka mutane 19, tare da jikata wasu ƙarin 342 a lokacin wani bikin sheƙe aya da matasa suka gudanar a garin Duisburg na yammacin ƙasar nan. Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ta ce da akwai bukatar zurfafa bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru. Cikin wani rahoto da ta wallafa a shafinta na intanet, mujallar nan ta Jamus mai suna Der Spiegel ta ce dandalin na faɗin da zai iya ɗaukar mutane dubu 250 ne. Amma kuma wannan adadin matasa ya ninka har sau shida waɗanda suka kwarara bikin na raya al'adu kiɗan zamani ta Techno. Shi wanda ya shirya bikin da akewa laƙabi da faretin soyayya ko kuma "Love Parade" dake gudana a kowace shekara, ya ce ba zai ƙara shirya shi ba, a wani mataki na karrama waɗanda suka rigamu gidan gaskiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal