Bala′in ambaliya a Pakistan | Labarai | DW | 07.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bala'in ambaliya a Pakistan

Pakistan ta nemi taimako sakamakon ambaliyar ruwa da ta rutsa da ita

default

Wasu da ke ƙoƙarin guje wa bala'in ambaliya.

Firaministan Pakistan, Yousuf Raza Gilani ya yi kira ga ƙasashen duniya da su taimaka wa al'umar ƙasarsa da ke fama da ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekaru 80. Hukumomin ba da agajin gaggawa a Pakistan sun ce yanzu haka akwai kimanin mutane miliyan biyu da wannan ambaliyar ta shafa, bayan mutane fiye da dubu 1600 da suka rasu a cikin makwanni biyu kenan. A jawabinsa ga al'uman duniya ta kafofin yaɗa labarai, Firaminista Gilani ya ce ƙudirin gwamnatinsa yanzu shi ne na sake matsugunai ga al'umar da wannan bala'i ya auka wa daga yankunan da suke zaune. Yanzu haka dai wannan ƙoƙari na ci gaba da fuskantar matsalar yanayi da ke kawo cikas ga ayyukan jiragen saman sojin Pakistan da na Amirka da ke kai kayan agaji zuwa yankin Swat da ambaliyar ruwan ta fi ƙamari.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas