1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bala'in ambaliya a Afirka

August 11, 2010

Ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/OitH
Tasirin ambaliyar ruwaHoto: DW

Yawan mutane da suka rasa rayukansu a bala'in ambaliyar ruwa da ta addabi wasu ƙasashen Afirka ya tasamma 120. Shirin Abinci ta Duniya(WFP) da ya bayar da wannan sanarwa ya ce ruwan sama kaman da bakin ƙwarya da ake fiskanta a ƙasashen yammaci da kuma tsakiyar Afirka na ci gaba da haifar da illoli da dama ciki har da mace-macen yara ƙanana da kuma mata masu juna biyu.

Ƙasashen da suka haɗa da jamhuriyar Niger, da Chadi da kuma Kamaru na daga cikin waɗanda ambaliyar da lalata gonaki da kuma matsugunai a cikinsu. WFP ko kuma PAM ta nuna fargaba game da ƙarancin abinci da ambaliyar za ta haifar nan gaba. Wannan ambaliyar ta haifar da mutuwan mutane 150 a arewacin Kamaru a cikin makonnin baya-bayannan. To amma Abdullahi Mahaman, mataimakin shugaban gundumar Blanguwa da ke arewacin Kamaru, ya ce gwamantin wannan ƙasa ta fara ɗaukar matakan hana yaɗuwar cutar amai da gudawa.Ƙwararru sun nunar da cewa sauyin yanayi na ɗaya daga cikin dalilan ambaliyar ruwa a waɗannan ƙasashe na Afirka baya ga gine-gine ba bisa ƙa'ida ba.

Mawallafi: Mahamadou Awal Balarabe

Edita: Halima Balaraba Abbas