1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Balahirar dake wanzuwa a yankin gabas ta tsakiya

Ibrahim SaniAugust 1, 2006

Kungiyyar Eu tayi Allah wadai da sabon matakin da majalisar tsaron Israela ta dauka

https://p.dw.com/p/BvTP
Hoto: AP

A cewar rahotanni a yau talata an shiga rana ta uku ke nan dangane da ci gaba da fafatawa da dakarun sojin Israela keyi da dakarun kungiyyar Hizbullah, a yankunan Taibe da Adaisseh da kuma Kfaf Kila dukkan su dake kudancin Labanon.

A yayin da kuwa ake cikin wannan hali a waje daya kuma tuni jami´an zartarwar majalisar tsaron kasar ta Israela ta bawa sojin ta umarnin fadada hare haren da suke kaiwa izuwa kudancin kasar ta Lebanon da zummar fatattakar dakarun sojin na Hizbullah.

A cewar bayanai, kasar ta Israela zata aiwatar da wannan aikin ne ta hanyar amfani da sojin ta da suka kware da yakin kasa.

A game da hasashen da Kasar ta Israela keyi na tunanin watakila kasar Syria ka iya taimakawa kungiyyar ta Hizbulla da makamai, tuni sojojin saman kasar suka yi ruwan bama bamai a kann wata cibiyar ajiye makamai ta kasar a hannu daya kuma da ragargaza hanyar data hada kasar ta Lebanon da Syria daga can iyakar arewa maso gabashin kasar ta Lebanon.

Bisa wannan al´amari kuwa tuni Shugaba Bashir Al Assad na Syria ya umarci dakarun sojin sa dasu kasance cikin shirin ko ta kwana,dangane da abin da ka iya barkewa na dangane da fada a yankin.

Game kuwa da matakin da majalisar tsaron kasar ta Israela ta dauka, kafafen yada labaru tuni suka rawaito Kasar Finland wacce a yanzu haka ke rike da mukamin karba karba na kungiyyar Tarayyar Turai, na Allah wadai da wannan mataki na kara kutsa kai izuwa kudancin kasar ta Lebanon.

Aiwatar da wannan mataki a cewar kasar ta Finland babu abin da zai haifar illa kara karuwar tsageru da zasu marawa yan kungiyyar ta Hizbullah baya a yankin na gabas ta tsakiya.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin kaqsashen Larabawa da kuma kungiyyar ta Eu na a kann bakan su ne na daukar matakan kawo karshen wannan balahira, to amma a waje daya kasar Amurka ta ke kasa kasar cewa dole ne a cimma yarjejeniya ta tsagaitawa da bude wuta akan iyakar kasashen biyu, don hakan ya zamo kariya daga duk wata barazana da kungiyyar ta Hizbullah zata yiwa kasar ta Israela a nan gaba.

Daga kuwa tun lokacin da aka fara wannan balahira izuwa yanzu kusan makonni uku, bayanai sun tabbatar da cewa yan Lebanon a kalla 605 ne suka rasa rayukan su , to amma ministan lafiya na kasar yace sun kai 750, ciki har da gawarwaki da har yanzu suke karkashin kasa.

A daya hannun kuma an kiyasta cewa Bani yahudu 51 ne suma suka rasa rayukan nasu.

Ya zuwa yanzu dai tuni Mdd ta dage lokacin ci gaba da tattauna matakin aikewa da dakarun Mdd izuwa yankunan da ake wannan balahira, har zuwa mako mai zuwa, wanda kafin lokacin ake sa ran shawo kann al´amarin ta hanyar diplomasiyya.