1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haurekusan 100 sun isa tsibirin Canary na kasar Spain

September 6, 2006
https://p.dw.com/p/BukZ

Rahotanni daga Spain na nuni da cewa kusan bakin haure 100 ne daga kasashen yammacin Africa suka isa tsibirin Canary na wannan kasa.

Koda a jiya a cewar rahotanni, sai da wasu bakin hauren 900 suka isa wannan tsibiri na Canary.

Ya zuwa yanzu dai tuni mahukuntan wannan tsibiri suka daukaka kiran neman taimako daga gwamnatin ta Spain da kuma kungiyyar Eu, don shawo kann wannan matsala.

Neman tallafin dai yazo ne, bayan da bakin hauren dubu 22 suka samu isa tsibirin a wannan shekara da muke ciki, wanda ya rubanya har sau hudu a shekarar data gabata.

Kafafen yada labaru sun rawaito Mahukuntan Spain na sukar lamirin kasashen Africa da rashin yin wani katabus, na hana bakin hauren shigowa izuwa nahiyar ta turai.

Rahotanni dai sun nunar da cewa yanzu haka dai, kasashe irin su Spain da Italiya da kuma Fransa na shirin kaddamar da wani shiri na hadin giwa da kungiyyar ta Eu zata yaki wannan matsala ta bakin hauren a lokacin taron kungiyyar Eu a Kasar Finland.