Bakin Haure | Siyasa | DW | 12.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bakin Haure

Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai na ci gaba da fama da matsalar bakin haure duk da tsauraran matakai da take dauka domin tsaron iyakokin kasashenta na gabacin Turai

Ita dai Kungiyar Tarayyar Turai ta kashe makudan kudi wajen kirkiro fasahohi da injunan da take amfani da su domin hana tuttudowar haramtattun baki da manema mafakar siyasa zuwa kasashenta. A baya ga haka matakai na soja da ake dauka misali a yankin Balkan da kuma shirye-shiryen taimakon raya kasa da aka gabatar sun taimaka aka fara samun sassaucin tuttudowar dubban daruruwan manema-mafakar siyasar da kuma shawo kan wadansu daga cikinsu domin komawa gida. Amma fa da zarar mutum ya fita daga iyakokin kasashen kungiyar a bangaren gabaci zai tarar da yake-yake da rikice-rikice dabam-dabam kama daga Chechniya da Georigiya zuwa Azerbijan da Nagorni Karabach da Armeniya. A nan ba sai an yi batu a game da kasashen Irak da Afghanistan da ma Yankin Gabas ta Tsakiya baki daya ba.

Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda Kurdawa da Checheniyawa ke bakin kokarinsu wajen shigowa yammacin Turai domin neman mafaka da kare makomar rayuwarsu. Wani sabon ci gaba da aka samu dangane da matsalar guje-gujen hijirar kuma shi ne yadda ake dada samun karuwar yawan makaurata daga yankunan gabaci da kudancin Asiya, musamman ma daga kasashen China da Indiya. Sai dai kuma wadannan makaurata, ba manufarsu ce su yi zama na dindidin a harabar Jamus ba. Galibi su kan yada zango ne a kasar a kokarinsu na neman zarcewa zuwa Birtaniya ko arewacin Amurka. Wani abin dake taimakawa kuwa shi ne rashin saukin samun bisar kasar Rasha, inda makauratan kan fara ya da zango a Mosko kafin su karaso zuwa yammacin Turai. Kungiyoyi na ‚yan baranda dake safarar babakin hauren suna da wakilansu a cikin gida da ketare, wadanda ke sa ido akan al’amura ke gudana. Wadannan kungiyoyi sun kunshi tsaffin ‚yan kaka-gida ne, wadanda ke da cikakkiyar masaniya a game da yanayin shige-da-ficen saboda su kansu ta kan irin wannan hanya suka bi kafin su haye tudun na-tsira. Yawa-yawancinsu sun shiga harkar cinikayya ta ketare ko kuma sun bude gidajen abinci suke kuma bakin kokarinsu wajen shigo da sauran danginsu ko kuma wasu bakin dabam akan farashi mai tsadar gaske a kasashen da suka samu gindin-zama. To sai dai kuma a lokacin da yake bayani wani da ake kira Matthias Neske daga cibiyar nazarin manufofin kaka-gida ta nahiyar Turai, wanda kuma yayi tsawon shekaru masu tarin yawa yana bin diddigin wannan matsala ya nuna cewar, wadannan ‚yan baranda ko da yake suna cin kazamar riba, amma fa ba su da wata masaniya a game da cewar wannan aikin nasu mugun laifi ne ba. A maimakon haka ma wasu daga cikinsu na tattare da imanin cewar wani gagarumin taimako ne suke bayar wa ga ‚yan-uwa da sauran dangi da abokansu na arziki ta hanyar share musu hanyar shigowa kasashe masu wadatar arziki domin kyautata makomar jin dadin rayuwarsu. Amma wannan maganar ba ta shafi masu fatacin mata ko yara kanana da ake tilasta musu karuwanci da ayyuka na bauta ko kuma masu safarar miyagun kwayoyi ba. Wadannan mutane ne dake sane da miyagun laifukan da suke aikatawa.