Bakin haure a Morokko | Siyasa | DW | 11.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bakin haure a Morokko

Bakin haure na fama da kaka-nika-yi a Morokko

Bakin haure

Bakin haure

Wadannan bakin haure daga kasashe daban-daban na yammacin Afurka su kann shafe kwanaki masu yawa suna taka sayyada akan hanyarsu ta kokarin shigowa nahiyar Turai. Wasu daga cikinsu danginsu ne suka yi karo-karo domin taimaka wa akalla daya daga cikinsu ya shigo nahiyar Turai Albashi ko ya samu aikin yi ta yadda zai taimaka wa sauran ‚yan uwa. Daya daga cikin bakin hauren da kaddara ta rutsa da su, mai suna Alfissine Icampo daga kasar Mali, wanda jami’an tsaron Maroko suka cafke shi aka kuma shirya komawa da shi gida a yau talata, yayi nuni da irin radadin dake tattare a zuciyarsa yanzu haka, saboda ya baro matarsa da ‚ya’yansu biyu cikin hali na kaka-nika-yi kuma a yanzun bai san abin da zai fada wa matar tasa idan ya isa gida ba. Ya ce bayan da suka cafke shi, jami’an tsaron na Maroko sai da suka lallasa shi, sannan suka karbe ‚yan kudaden dake hannunsa kafin su tasa keyarsa zuwa wani yanki na hamada. Shi dai Alfissine daya ne daga cikin dubban dubatar ‚yan Afrika daga kasashen Senegal, Mali, Guinea, Nijeriya, Sierra Leone, Togo, kazalika har da ‚yan kasashen Latin Amurka da Pakistan. Wasu ‚yan baranda ne ke satar hanyar fasakwabrin wadannan bakin haure zuwa Maroko akan makudan kudi. Tun dai misalin shekaru 25 da suka wuce kasashe da dama na Afurka ke fama da koma bayan tattalin arziki kuma da yawa daga al’umar Afurka na fama da radadin talauci fiye da iyayensu a zamanin baya. Wannan matsalar kuwa, ba kawai yake-yake na basasa da cin hanci na magabatan kasashen Afurka ne ummal’aba’isinta ba, kazalika dangantakar ciniki ta kasa da kasa tana taka muhimmiyar rawa wajen dankwafar da tattalin arzikin wannan nahiya. A cikin shekaru gwamman da suka wuce kasashe masu tasowa masu dogara kacokam akan cinikin danyyun kayayyaki sun fuskanci faduwar farashin wadannan albarkatun kasa dake samar musu da kudaden musaya na ketare. Wani abin dake tsawwala matsalar kasashen ma shi ne matakin karya farashin amfanin noma da kasashe masu ci gaban masana’antu ke dauka wanda ke gurgunta matsayin manoma daga kasashe masu tasowa a kasuwannin duniya. Ire-Iren wadannan manoma da direbobin tasi da sauran masu sana’o’i na hannu, su ne kann kama hanyarsu ta zuwa nan nahiyar Turai a fafutukar kyautata makomar rayuwarsu da iyalansu sakamakon radadin talaucin da suke fama da shi a gida. A lokacin da yake bayani game da mawuyacin halin da ya samu kansa a cikin bayan rasuwar iyayensa, wani da ake kira Patrick daga kasar Gambiya mai shekaru 28 da haifuwa da kuma ‚yan uwansa su bakwai cewa yayi:

Idan na samu ikon kama aiki a nahiyar Turai zan samu kafar daukar nauyin ilimantar da kanne na. Bayan rasuwar iyayenmu na danka su a hannu makobtanmu na kuma roke su da su kula da makomarsu, kafin in baro gida.

Wasu daga cikin ‚yan gudun hijirar kann yi asarar rayukansu a hamadar sahara sakamakon kishirwa. Kuma wadanda suka tsallake rijiya daga cikinsu har suka isa kasar Moroko sai fuskanci wata sabuwar kalubala. Su kann shiga tsoron kada ‚yan sanda su cafke su, wadanda a nasu bangaren ke neman toshiyar baki, kuma wanda bai da iko sai a tasa keyarsa zuwa Oujda dake bakin iyakar kasar Aljeriya ko kuma a bar shi a cikin hali na kaka-nika-yi a hamada, inda aka ce kimanin mutane 30 suka yi asarar rayukansu a ‚yan kwanakin baya-bayan nan. Su dai jami’an tsaron Maroko ba abin dake ci musu tuwo a kwarya game da haka.