Bakin haure 102 daga Senegal zuwa Spain sun bace a cikin taku | Labarai | DW | 17.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure 102 daga Senegal zuwa Spain sun bace a cikin taku

Masunya a Senegal sun ceto wasu bakin haure na kasar su 25 da suka yi kokarin kaiwa ga yankin kasar Spain ta ruwa. Har yanzu kuma ba´a ga sauran mutum 102 ba. Wasu daga cikin wadanda aka ceto sun ce tun a ranar 3 ga watannan na desamba kimanin mutane 127 suka fara wannan tafiya mai hadari a cikin wani kwale-kwale. Suka ce sun tashi ne daga yankin Bolongne dake kudancin Senegal inda suka doshi tsibirin Canary dake karkashin kasar Spain. Yanzu haka an kai wadanda aka ceto wani asibiti dake garin Saint Louis.