Baki ma′aikata a Jamus | Zamantakewa | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Baki ma'aikata a Jamus

Tun fiye da shekaru 50 ke nan da aka kulla wata yarjejeniya ta shigo da baki ma'aikata zuwa nan Jamus, don su cike gibin da aka samu na karancin ma'aikata, a lokacin sake gina kasar bayan kayen da ta sha a karshen yakin duniya na biyu.

Kulla farkon yarjejeniyar shigo da baki ma'aikata daga Italiya zuwa nan Jamus, a birnin Rom a shekarar 1955.

Kulla farkon yarjejeniyar shigo da baki ma'aikata daga Italiya zuwa nan Jamus, a birnin Rom a shekarar 1955.

A lokacin da aka sanya hannu kan yarjerjeniyar shigo da ma’aikata baki a nan Jamus, shekaru 50 da suka wuce, halin rayuwa a Jamus daban yake da na yanzu. Jamus, a wannan lokacin, na ta fama ne da sakamakon bala’in yakin duniya biyu, wanda aka gama a shekarar 1945. Wannan yakin dai, shi ne ya janyo raba Jamus da aka yi a sassa biyu, wato Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma. Ita Jamus ta Gabas, ta kasance ne karkashin mulkin gurguzu irin na tarayyar Soviyet, wadda ta mamaye wannan yankin ta sanya shi kuma karkashin angizonta. Ita ko Jamus ta Yamma, sai ta fada a hannun rukunin kawance da Amirka ke yi wa jagoranci. Tallafin da Amirka ta ba ta a wannan lokacin ne ya ba ta damar iya bunkasa tattalin arzikinta, fiye da tsammani. A yunkurin da take yi na sake gina kasar daga tarkacen bamabaman da aka jejjefa wa biranenta a yakin duniya na biyu, gwamnatin Jamus ta Yamma, ta kasance tana bukatar dimbin yawan ma’aikata, fiye da wadanda take da su a cikin gida, musamman a fannonin hako ma’adinai da noma da masana’antu da gine-gine. Sabili da haka ne ta yanke shawarar shigo da ma’aikata baki don cike wannan gibin. Farkon matakin da ta dauka ne kulla yarjejeniya da Italiya, wadda aka rattaba hannu a kai a wani gagarumin bikin da aka yi a birnin Rom, a ran 20 ga watan Disamban 1955.

Duk da haka, wannan yarjejeniyar ba ta iya ta biya bukatar da ake yi na dimbin yawan ma’aikata ba. Sabili da haka ne aka tsai da shawarar kulla wasu yarjejeniyoyin kuma da wasu kasashe bayan Italiyan. A shekarar 1960 aka kulla irin wannan yarjejeniyar da kasashen Girka da na Spain. Daga baya ne kuma aka yada shirin zuwa Turkiyya, da Tunesiya, da Maroko, da Portugal da Yugoslaviya. Wannan lokacin dai, shi ne farkon muhimmiyar kaurar ma’aikata zuwa Jamus, a tarihinta. A cikin shekarar 1964 ne aka tarbi ma’aikaci na miliyan daya a tashar jirgin Kolon, inda aka shirya masa wata liyafa ta musamman, har da ba shi kyautar babur, abin da ke alamta yabon da ake yi wa kwazon da baki ma’aikata suka nuna wajen gudanad da ayyukansu, a cikin shirye-shiryen farfado da tattalin arzikin Jamus.

To yau, shekaru 50 bayan kulla wannan yarjejeniyar, ra’ayoyi sun bambanta game da kasancewar baki a nan Jamus. Akwai wadanda har ila yau ke jinjina wa bakin, game da gudummowar da suka bayar wajen sake farfado da tattalin arzikin Jamus. Amma akwai kuma wadanda ke ganin cewa, wannan matakin ya haifad da wasu matsalolin da ake huskanta a halin yanzu, wato shekaru 50 bayan daukarsa. A daura da yadda aka zata a da din dai, ma’aikata da dama ne suka yi kaka gida a Jamus, saboda kyakyawan halin rayuwar da suka samu da kuma a wasu lokutan, saboda bukatar da masana’antunsu ke yi na su ci gaba da aikin. Ta hakan ne dai, mafi yawa daga cikinsu, musamman Turkawa, suka yi ta shigo da iyalansu, har aka wayi gari yau, zuri’arsu ta bunkasa ta kai ga jikoki. A halin yanzu dai yawansu a nan Jamus ya kai miliyan biyu, abin da ya sanya su a kan gaba, na duk rukunan baki mazauna nan kasar.

Ko’ina a nan Jamus a yau dai, za a iya ganin rumfunan sayad da abincin nan „Döner Kebap“ na Turkawa, ko kuma kantunan sayad da Pizza na Italiyawa. Sai dai har ila yau, da yawa daga cikin bakin ba su saje sun rungumi halin rayuwar Jamusawa ba. Hakan kuwa ya sa `ya`yan da suka haifa, ba su iya yaren Jamusancin sosai ba, abin da kuma ke janyo musu cikas wajen koyon sana’o’i ko kuma a makarantu. A kasuwar kwadago ma, su ne matsalar rashin aikin yi ta fi shafa.

Wannan halin dai, shi ne abin da ya fi kalubalantar `yan siyasan Jamus a halin yanzu. Saboda, an tabbatar da cewa, idan ba su iya shawo kan wannan cinkoson matasa marasa cikakken ilimi da kuma guraban aikin yi a cikin wani lokaci matsakaici ba, to za a wayi gari, a huskanci mummunar tarzoma irin wadda ta auku a makwabciyar yamma ta Jamus din, wato Faransa.