Bakar Fata A Daular Jamus Ta Uku | Siyasa | DW | 18.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bakar Fata A Daular Jamus Ta Uku

Bakar fatar da suka shigo Jamus a zamanin da kasar ke mulkin mallaka a ketare sun dandani kudarsu a matakan gallazawa da cin mutuncin da 'yan Nazi suka rika dauka a karkashin manufofinsu na wariyar jinsi

Wani dan wasan kwaikwayo da ake kira Theodor Michael ya kasance daya daga cikin wadannan ‚yan ruwa biyu da suka fuskanci gallazawa da cin mutunci a hannun ‚yan Nazin-Hitler. A shekarar 1925 aka haifi Theodor Michael a birnin Berlin. Mahaifinsa daga kasar Kamaru ya shigo Jamus ne a daidai lokacin da kasar take kan hanyar yada angizonta na mulkin mallaka, inda yayi kaka-gida ya kuma auri wata Bajamushiya. Daya daga cikin dalilan da suka sanya aka shiga kyamar wadannan ‚yan ruwa biyu shi ne rawar da bakar fata suka taka a sojan kasar Faransa wajen mamayar wasu yankunan Jamus a lokacin yakin duniya na farko. Akan tara wadannan bakar fata a gandayen namun-daji domin zama abin kallo a karkashin abin da aka kira wai baje kolin mulkin mallaka. Muzantawar ta dada yin muni bayan da Hitler ya dare kan karagar mulki, inda suka wayi gari ba su da wani ‚yanci a kasar. A matsayinsu na bakar fata ko ruwa biyu, wadannan yara ba su da ikon halartar makarantu na gaba da sakandare, kuma daga bisani suka wayi gari ba su da hakkin zama ‚yan kasa, ballantana a yi batu a game da kama wata sana’ar da zata taimaka musu wajen kyautata makomar rayuwarsu. Theodor Michael ya ce iyayensa ba su shaidar da wannan muzantawa da dokokin da aka gabatar don kayyade 'yancinsu ba. Saboda shi kansa mahaifinsa ya rasu ne a shekarar 1934 bayan da mahaifiyarsa ta fara mutuwa tun da farkon fari. Dukkan bakar fata sun daina fita saboda tsoron makomar rayuwarsu, sai matansu ne kawai ke fita aiki domin samun kudaden shiga. Wata harkar da ta dan taimaka wajen samun aikin yi ga ‚yan usulin Afurka ita ce ta harhada fina-finan silima, inda akan daukesu tamkar ‚yan rakiya a wasu fina-finan da suka jibanci nahiyar ko kuma al’amuran mulkin mallaka ko farfagandar siyasa. Ire-iren wadannan finafinai kimanin 100 aka harhada kawo ya zuwa shekarar 1942. A wadannan finafinai zaka tarar da bakar fata na biyayya sau da kafa ga iyayen gijinsa farar fata. Shi kansa Theodor Michael ya sha shiga ana damawa da shi a irin wadannan finafinai. A shekarar 1943 ne aka dakatar da wadannan finafinai ko da yake shi dattijon, wanda Allah Ya taimake shi ya tsallake rijiya da baya, har yau ya kan shiga ana damawa da shi a wasannin dirama a gidajen wasannin kwaikwayo.