1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baje kolin Littattafai na duniya a Frankfurt

October 8, 2010

Kasashen duniya daban daban ne ke ci gaba da halartar kasuwar baje kolin Littattafai mafi girma a duniya, wanda birnin Frankfurt na kasar Jamus ke karbar bakuncin ta.

https://p.dw.com/p/PZPM
Hoto: DW

Kasuwar baje kolin Littattafan na duniya wanda birnin Frankfurt na nan Jamus ke karbar bakuncin ta a duk shekara, kimanin mawallafa 7,500 ne suka baje littattafan su, wadanda kuma suka fito daga kasashen duniya 111.

Ita kanta kasuwar dai ba ta sayar da littatafan kai tsaye bace, amma dandali ne da ke baiwa kamfanonin buga littattafai damar kulla yarjejeniyoyi a tsakanin su, da sanin harkokin hada hadar littattafai da kuma cinikayyar su.

Eröffnung der Buchmesse Frankfurt - Kirchner und Westerwelle
Hoto: picture alliance/dpa

Kimanin mutane dubu biyu da 900 ne suka halarci baje kolin littattfan daya gudana a birnin Frankfurt a shekarar da ta gabata, galibin su kuma Jamusawan da ke hankoron saduwa da mawallafa da kuma littattafan da ake sa ran fitar su a nan gaba.

Frankfurt Buchmesse 2010 Lizenzverkauf
Hoto: DW/Petra Lambeck

A wannan karon Argentina ce babbar bakuwa a kasuwar, inda shugabar kasar ta Argentina Cristina Fernandez Kirchner ta bayyanawa mahalarta baje kolin cewar kasar ta fa ba tayar baya bace wajen kyawawan al'adu da kuma mawallafan da ke tasowa:

"Argentina ba za ta taba zama kasa ta zamanin da wai kawai kwaskwarima aka yi mata ba, domin tana da tarihin ta na tsawon shekaru 200n da suka gabata, wanda ke tattare da turuka da kuma rigingimun da marubutan mu ke bayyanawa a cikin wallafe - wallafen su."

Galibin mawallafan da ke halartar baje kolin dai, suna burin kulla yarjejeniyar da ta shafi ba su 'yancin yin fassarar wasu littattafan da aka rubuta ne musamman daga manyan mawallafa cikin harshen turanci, wadanda suka mamaye harkar cinikayyar littattafai a duniya.

A cewar shugaban kungiyar masu hada hadar littattafai a nan Jamus Gottfried Honnefelder, mawallafa sun amsa kiran shugabar Argentinar da ta kaddamar da kasuwar, na bayar da himma sosai ga fassara littattafan da marubuta daga kasar ta suka wallafa:

"Jamusawa mawallafa sun yi kyakkyawar amsa kiran babbar bakuwa. Kusan wallafe - wallafe 220 ne suka fassara daga harshen Spaniyancin da Argentina ke yin amfani da shi ya zuwa Jamusanci, 117 daga cikin su kuma sun shafi tatsuniyoyi ne da alma'ra."

Sai dai duk da irin karance - karancen littattafan da jama'a ke yi, mawallafa na nuna fagabar cewar, akwai yiwuwar littattafan da ake sanyawa a cikin yanar gizo suna janyo koma baya ga sha'anin sayan wadanda aka buga, domin a cewar su wadanda ake sayarwa ta hanyar yanar gizo sun fi araha sosai, abinda suke ganin zai sa mutane su fi mayar da hankali ga sayan irin wannan nau'i na littattafai.

Frankfurter Buchmesse 2010
Hoto: DW

Darektan kasuwar baje kolin littattafai na birnin Frankfurt Jürgen Boos ya yi kira ga mawallafa da a kullum su kasance masu hangen nesa:

" Kira na shi ne mu saurari gaba ta yadda al'amura za su ci gaba da motsi. Abin farin ciki ne ganin yadda ake kokarin fuskantar wata sabuwar alkibla, ko da yake ba mu san makomar tafiyar ta mu ba, amma ga alamu hanya ce madaidaciya wadda za ta ba mu dama iri daban daban."

Kasuwar baje kolin littatafai mafi girma a duniya baki dayan a birnin Frankfurt na nan Jamus, wadda ta fara ci a ranar talata 5 ga watan Oktoba, za ta ci gaba da gudana har ya zuwa ranar 10 ga watan na Oktoba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas