Baje kolin albarkatun yawon bude ido a Jamus | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baje kolin albarkatun yawon bude ido a Jamus

An bude bikin baje kolin albarkatun yawon bude ido na kasashen duniya a birnin Berlin na nan Jamus.

A bana dai an samu baje albarkatu iri dabam dabam na yawon bude ido kusan 11,000 daga kasashe 184.

A wannan shekara kasar Indiya ce akak kebewa sashe na musamman inda zata baje albarkatunta na yawon bude ido.

Wajen bude bikin a daren jiya ministan tattalin arziki na Jamus Michael Glos yace kasar Jamus ke kann gaba wajen samun bakin na yawon shakatawa a shekarar data gabata.