Bajamushen da ake garkuwa da shi a Afghanistan na fama da rashin lafiya | Labarai | DW | 24.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bajamushen da ake garkuwa da shi a Afghanistan na fama da rashin lafiya

Ana ci-gaba da tattaunawa da nufin samun sakin ´yan KTK 23 da ake garkuwa da su a Afghanistan duk da cikar sabon wa´adin da ´yan Taliban suka bayar. Tare da taimakon wata tawaga ta shugabannin kabilu da na addini yanzu haka masu shiga tsakani na KTK na tattaunawa da ´yan Taliban a lardin Ghazni. Wasu rahotanni da ba´a tabbatar da su ba na cewar ´yan takifen sun bukaci da a ba su makudan kudade kafin su saki mutanen da suke garkuwa da su. A wani labarin kuma Bajamushuen nan dake hannun ´yan Taliban tun a makon jiya yana fama da rashin lafiya ba tare da an ba shi damar ganin likita ba. Gwamnati a birnin Berlin ta tashi haikan don ganin an sako dan kasar na ta. SGJ Angela Merkel ta fadawa majalisar ministoci cewa wani kwamitin da aka kafa na aiki ba dare ba rana don ganin an sako Bajamushen.