1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bajamushe a Wurin Aikinsa

April 22, 2010

Ku koyi sanin Jamus ta hanyar rayuwar al´ummomin dake zaune a sassa daban-daban na ƙasar. Deutsche Welle ta tura wakilai kowane lungu, da kowane saƙo na ƙasar Jamus, domin tattaunawa da ma´aikata.

https://p.dw.com/p/N2gH
Kudu da arewa, gabas da yamma, ma´aikata na ba da labarin rayuwarsu ta yau da kullum, da kuma bururukan dake cikin zukatansu. Tare da waɗannan rahotanni masu taken „Gesichter Deutschlands“ ko "Bajamushe a Wurin Aikinsa" za ku ji bayanai daga tushe, game da yanayin aiki a Jamus da suffofin rayuwar Bajamushe. Za ku iya sauraron rahotanni na harshen Hausa a cikin shirye-shiryenmu na yamma kowace Talata da Alhamis. Sannan za ku iya karanta labarin da harsunan Faransanci da Turanci a cikin wannan shafi.