1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci a cibiyar 'yan hijira a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
May 23, 2018

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Jamus a wannan rana ta Laraba ta ba da umarni na a tsayar da bayar da takardun neman mafakar siyasa a wani ofishi na hukumar da ke kula da harkokin 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2yD26
Bundesamt für Migration Schild Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Karmann

Masu gabatar da kara sun kaddamar da bincike na badakalar cin hanci da rashawa a ofishin tsohon shugaban sashin kula da karbar baki da 'yan gudun hijira (BAMF) bisa zargin ba da takardar mafakar siyasa ga mutane 1,200 ta hanyar da ba ta dace ba a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016.

A cewar ministan harkokin cikin gidan Jamus Horst Seehofer cibiyar karbar 'yan gudun hijirar da ke a Bremen ta zubar da kimar da take da ita sakamakon badakalar cin hanci da aka gano a hanyoyin da ake bi wajen ba da mafakar siyasa a wannan cibiya.

Bayan dai da Jamus ta bude kofarta ga 'yan gudun hijira a shekarar 2015. Batun na 'yan gudun hijira ya kasance lamari da ke daukar hankali a tsakanin 'yan siyasar ta Jamus.