Bada tallafi ga fursunoni a Malawi
September 27, 2017Cunkoson mutane a gidan yarin kasar Malawi inda fursunoni kan shafe shekaru ba tare da an yanke musu hukunci ba to rashin adalci ne a tsarin shari'a in ji Steve Sikwese daya daga cikin wadanda ke aikin samarwa fursunoni yanci karkashin wata kungiya mai zama kanta mai suna Paralegal Advisory Service Institute (PASI) kungiyar ta na kai wa fursunonin ziyara tare da sauraron kokensu kafin daga bisani ta bi hanyar fitar da su daga gidan yarin,
A cewar Steve, fursunonin da dama na daure ne saboda laifi na sace-sace wanda tsanannin talauci ya haddasa, in har sun duba sun kuma tabbatar laifin ba wani abun a zo a gani bane sai su shiga tsakani ta hanyar yin belinsu ko su biya wa fursunonin kudin tara, amman wani abin takaici ma akwai fursunonin da ake tsare da su bisa zargi ba tare da an tabbatar da cewa sun aikata laifin ba, a cewar Steve wannan na daga cikin dalilan da ya sa shi da abokinsa Clifford Msiska kafa kungiyar ta PASI.
Mutane da dama ne dai suka ci gajiyar shirin da wannan kungiya ta PASI ke yi cikinsu kuuwa har da Philipina ta bar gidan yari a shekaru biyun da suka gabata. Namijin kokarin da wannan kungiyar ke yi ya sa an sami raguwar cunkoson fursunoni a gidajen yarin kasar ta Malawi ganin yadda Steve da sauran abokan aikinsa suka yi nasarar taimaka wa dubban fursunoni samun yanci amman ta hanyar bin dokokin kasar da tsari na shari'a, bisa wadannan nasarori na kungiyar ta PASI wasu kasashen Afrika kamar su Uganda da Kenya sun soma yunkurin na aiki da wannan salo don tabbatar da adalci a kasa.