Badaƙalar turawan Faransa ta sace ƙananan yara | Labarai | DW | 30.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badaƙalar turawan Faransa ta sace ƙananan yara

Hukumomin shariá a ƙasar Chadi sun shirya gurfanar da turawan nan tara yan kasar Faransa a gaban kotun waɗanda suka yi yunƙurin sace wasu ƙananan yara fiye da ɗari ɗaya da kuma ficewa da su daga ƙasar Chadi. Lauya mai gabatar da ƙara ya shaidawa yan jarida cewa zaá kuma a tuhumi wasu matuƙan jirgin sama su bakwai yan ƙasar Spain tare da wasu yan ƙasar Chadi biyu da laifin haɗin baki domin aiwatar da wannan baƙar aniya . An tsare su ne a ranar alhamis da ta wuce a yayin da suke ƙoƙarin tashi daga birnin Abeche. Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jamiái na wata ƙungiyar agaji mai suna Zoes Ark. Ƙungiyar tace manufar su ita ce taimakawa ƙananan yaran marayu waɗanda suka fito daga yankin Dafur na ƙasar Sudan dake fama da rikici. Sai dai kuma hukumar kula da ƙananan yara ta majalisar ɗinkin duniya UNICEF tace wasu daga cikin yaran sun shaida mata cewa sun fito ne daga wasu ƙauyuka na ƙasar Chadi kuma iyayen su suna nan a raye.